IQNA

Ministan kula da harkokin addini na Aljeriya ya yi alkawali na  gaggauta aikin gina Masallacin Qutb

17:37 - September 28, 2023
Lambar Labari: 3489890
Algiers (IQNA) Ministan kula da harkokin addini na kasar Aljeriya ya sanar da cewa, ana kokarin kammala babban masallacin Qutb da ke birnin Tibazah mai tarihi tare da hadin gwiwar hukumomin kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Horizons cewa, Youssef Belmahdi, ministan kula da harkokin addini na kasar Aljeriya, ya jaddada cewa, tare da hadin gwiwar hukumomin lardin Tibazah, ana kokarin rage wa'adin kammala aikin masallacin Qutb na wannan birni.

A gefen ziyararsa ta kasuwanci a lardin Tibaze, Balmehdi ya yi bayani don duba yadda aikin ke gudana da kuma cikas ga ci gaban aikin gina masallacin Qutb, wanda ya kai kashi 75% na kammala aikin.

Ya ce tare da hadin gwiwar gwamnan za a yi kokarin rage wa’adin gina wannan babban masallaci da kuma bude dakinsa na addu’o’in jama’a kafin watan Ramadan.

Belmahdi ya dauki masallacin Qutb a matsayin wani katafaren gini na addini kuma fitilar da za ta samar da ayyukan da suka wajaba ga muminai daidai da shirin gwamnati na fadada ayyukan ibada a kasar Aljeriya.

Wannan katafaren ginin zai dauki masu ibada maza 10,000 da mata masu ibada 1,200 kuma za a gina shi a kan kasa mai fadin murabba'in mita 15,000 kuma zai kasance da wasu wurare da dama.

An yi rajistar aikin gina wannan masallaci a shekarar 2011 kuma an fara aikin ne a shekarar 2012, amma a shekarar 2021 aka dakatar da aikin, kuma aka jinkirta aikin. Sauran ayyukan sun hada da shirya dakin sallah na maza na musamman da dakin mata, baya ga farfajiyar waje, da kuma babbar kubba da minare hudu.

Har ila yau, wannan masallacin ya hada da filin ajiye motoci mai karfin motoci 150, da bangaren ilimi da ya hada da dakin karatu, ajujuwa, dakin karatu, dakin cin abinci, da shaguna 7, da lambun waje mai ruwa da wuraren hutawa.

Masallacin Qutb wani bangare ne na shirin gwamnati da ya kunshi gina masallatai 10 a fadin kasar Aljeriya a cikin shekaru goma na farko na karni na 21. Yawan dakatarwar da aka yi na wannan aikin ya kai ga kawo karshen kwangilar da kamfanin ya yi nasara a shekarar 2011, kuma a shekarar 2021, an kulla yarjejeniya da wani kamfanin Turkiyya don sake fara aikin.

"Masallacin Qutb" yana yammacin birnin Tibaze a wani fili da ke kallon teku da kuma kusa da dandalin jama'ar birnin, kuma za a gina cibiyar al'adun muslunci da makarantar kur'ani a gefensa.

 

 

 

4171566

 

captcha